22 Oktoba 2020 - 12:39
​Faransa: An Dauki Matakan Tsaro Masu Tsanani A Masallatan Da Suke Kudancin Kasar

Masallatai a birane guda biyu daga kudancin kasar Faransa suna karkashin kula ta jami’an tsaron kasar Faransa don hana masu tsatsauran ra’ayin addini kai masu hare-hare.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa musulman kasar Faransa suna cikin damuwa a cikin yan kwanakin nan, saboda kisan wani malamin tarihi a kusa da birnin Paris babban birnin kasar.

Samuel Paty malamin tarihi ne a wata makaranta a birnin wanda ya sha nunawa dalibansa zane-zanen batanci ga manzon All..(s) a cikin ajinsa.

A ranar Jummar da ta gabata ce wani dalibinsa dan asalin kasar Chechnia kuma dan shekara 18 a duniya mai suna Abdullah Anzorov ya kasheshi kusa da makarantarsa.

Wannan ya tunzura mutanen kasar gudanar da zanga-zanga ta neman a yi masa adalci. Yansanda Farasna sun kashe Abdullahi jim kadan bayan da ya kashe malamin nasa.

342/